Examine Jesus’ Authority Honestly and Accept God’s Son
Welcome to Day 295 of our journey with Jesus. Today, we think about how we will respond to Jesus. The main truth for today is this: Jesus calls us to examine his authority honestly and accept God's Son rather than use questions to avoid him. Let’s begin.
Current details of the journeyView the calendar, Episode and passage
Jesus in Action
Mark 11:27–12:12
Step 5 of 5
Decide how you will respond to Jesus.
Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa. Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?” Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!” Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.” Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.” Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya. Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu. Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe. “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’ “Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’ Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin. “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini. Ubangiji ya yi wannan, ya kuma yi kyau a idanunmu’?” Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.
Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman RubutaccenIzini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. “Biblica” wani tambarin ne da aka yi wa rajista a ofishi Lamba Ƙerar da Tambari a Amurka ta hannun Biblica, Inc. Wanda aka yi amfani ta wurin samun izini. “Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc. Used with permission.
We have followed the question, the parable, the rejected Son, and the cornerstone; today the issue is whether we will answer honestly.
Do not stop at asking whether Jesus has authority. Ask what you will do if the evidence points toward an answer you did not want.
Let Questions Seek Truth.
Bring difficult questions to Jesus. Examine the Gospel carefully. Test claims rather than pretending. But refuse the kind of questioning that exists only to protect a conclusion already chosen.
Recognize the Rejected Stone.
The leaders reject Jesus, yet His quotation says rejection will not determine the final outcome. God makes the rejected stone the cornerstone.
Release the Need to Remain Judge.
The leaders approach Jesus as examiners of His credentials. The passage gradually exposes that they themselves are being examined by how they respond to God’s Son.
Answer Honestly.
Jesus does not demand intellectual dishonesty. He demands moral honesty. When investigation reaches a point where His claim is clear, continued neutrality is itself a response. Receive the cornerstone rather than building a life around refusing Him.
Episode 10 closes here with Jesus’ authority unmistakably contested as the journey moves toward the cross.
Consider this.
What response does Jesus require?
Take your next step
Respond honestly to Jesus rather than using investigation as a permanent substitute for decision.